Ba za a samu hakikanin zaman lafiya a kasar Syria ba, sai an tabbatar da hakkin dan Adam na jama'ar kasar, a cewar Hong Lei
Hukumar kula da hakkin dan Adam ta MDD ta bayar da wani rahoto a ranar 11 ga wata, inda ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Syria da masu adawar kasar dukkansu sun aikata laifin tada yaki da na take hakkin dan Adam, kamata ya yi a yanke hukunci ga wadanda suke da laifin. A yau Alhamis 12 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, ba za a samu hakikanin zaman lafiya a kasar Syria ba sai an tabbatar da hakkin dan Adam na jama'ar kasar.
Game da batun Syria, ya ce, abin dake gaban kome shi ne kalubalan dake gaban bangarori daban daban na kasar Syria na su tsagaita bude wuta cikin hanzari, da gudanar da taro na biyu na Geneva kan batun Syria don warware matsalar ta hanyar yin shawarwari. (Zainab)