in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan adawar Syria ta fara wata ziyara a nan kasar Sin
2013-09-10 20:26:10 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya bayyana a yau Talata cewa, wata tawagar 'yan adawar kasar Syria mai wakilai 6 ta fara wata ziyara a nan kasar Sin bisa goron gayyatar cibiyar koyar da harkokin kasashen waje ta kasar Sin.

Hong Lei ya shaidawa taron manema labarai cewa, yayin da tawagar ke nan kasar Sin, ana saran za ta gana da manyan jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin inda za su yi musayar ra'ayoyi, yana mai cewa, kasar Sin tana kokarin shiga tsakani da dukkan bangarorin da abin ya shafa game da batun Syria ta hanyar da ta dace.

Mr. Hong ya ce, har kullum kasar Sin tana ganin cewa, hanyar siyasa ita ce mafiya ga batun Syria, kuma kamata ya yi a yi amfani da wannan mataki, musamman a halin da ake ciki yanzu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China