Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya gana da takwaransa na kasar Syria a kwanakin baya, inda ya bada shawara cewa, kamata ya yi kasar Syria ta mika makamanta masu guba, domin a lalata su sannu a hankali a karkashin sa ido na kasashen duniya don magance yiwuwar daukar matakan soja kan kasar. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta nuna maraba da shawarar kasar Rasha.
Hong ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su yi la'akari da duk wani irin abin da zai taimaka wajen sassauta batun kasar Syria, warware rikicin kasar da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin. (Zainab)