in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ta amince da shawarar Rasha game da makamai masu guba
2013-09-11 12:11:21 cri
Shawarar da kasar Rasha ta gabatar game da batun makamai masu guba na kasar Syria, ta samu goyon baya daga kasashen duniya da dama, abin da ya yi kama da bullo da kyakkyawan yanayi yayin da ake gab da barkewar yaki a kasar Syria.

Firaministan kasar Syria, Wael al-Halaki ya bayyana a jiya Talata cewa, gwamnatin kasar na goyon bayan shawarar Rasha, kuma a shirye take ta yi aiki tare da ragowar kasashen duniya, don ganin an aiwatar da shawarwarin da zasu bada damar kaucewa barkewar yaki. Har ila yau Walid Al-Moualem, ministan harkokin wajen kasar Syria ya bayyana cewa, kasar sa na shirin fayyace wa kasar Rasha da MDD wurin da runbun ta na ajiye makaman yake, tare da amincewa yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba.

Ban da wannan kuma, a ranar 10 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya soke shawarwarin sirri, na gaggawa kan batun Syria da dukkan kasashe mambobin majalisar suka shirya gudanarwa a wannan rana. Sai dai ba a sanar a hakikanin dalilin hakan ba.

A dai wannan rana ne kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hong Lei, ya yi bayani a yayin taron manema labaru da aka saba yi, inda ya ce kasar Sin na goyon bayan shawarar Rasha game da batun makamai masu guba. Yace a koda yaushe kasarsa na adawa da yin amfani da makamai don magance matsalolin dake tsakanin kasa da kasa.

A nasa bangaren, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Marzieh Afkham cewa ya yi kasar sa na goyon bayan shawarar Rasha, na daukar matakan kaucewa shiga yaki a yankin. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China