Kasashe da dama za su amincewa da matakin soja da za a dauka kan Syria, in ji Amurka
Ran 7 ga wata, yayin taron manema labaran da aka yi cikin hadin gwiwa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius da takwaransa na kasar Amurka John Kerry a birnin Paris, Mr.Kerry ya nuna cewa, kasashe sama da 10 na shirya daukar matakin soja da za a dauka kan kasar Syria. Ya kuma nuna jin dadinsa kan goyon bayan da kasashen kungiyar Turai suka baiwa kasar Amurka kan wannan mataki a yayin taron ministocin kasashen waje da aka yi a birnin Vilnius. Mr. Fabius ya bayyana cewa, kasashen Faransa da Amurka sun fi son daukar matakan soja na gajeran lokaci tare da karya labaran dake bayyana cewa kasashen Amurka da Faransa suka shiga hali na saniyar ware cikin gamayyar kasa da kasa wajen daukar makatan soja kan kasar Syria.
Bugu da kari a wannan rana, darurruwan masu zanga zanga sun fito domin yin kira majalisar dokokin kasar Amurka dake birnin Washington da kuma gaban fadar White House da ta ki amincewa da daukar matakin soja kan kasar Siriya da shugaba Obama ke shirin dauka bisa dalilin matakan soja za su kara haddasa illa ga fararen hular kasar Syria da kuma janyo asarar kudade ga kasar Amurka wanda ta shiga cikin yake yake da dama cikin shekarun da suka wuce lamarin da ya gurgunta yanayin tattalin arzikin kasar da zaman rayuwar jama'a. (Maryam)