A kuma dai wannan rana ne takwaransa na kasar Syria, da har yanzu ke ziyara a Rasha, Walid Al-Moualem ke cewa Syria na maraba da shawarar Rasha, game da mai da nau'oin makamanta masu guba karkashin sa idon kasashen duniya.
A nasa bangare babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yi bayani a wannan rana cewa, yana maraba da wannan shawarar da Rasha ta gabatar, kana ya yi la'akari da ba da shawara ga kwamitin sulhu, da nufin bukatar Syria ta aika da makamai masu guba zuwa wani wurin da ya dace, don lalata su.
Shi kuwa shugaba Barack Obama na kasar Amurka cewa ya yi, shawarar mayar da makamai masu guba na Syria karkashin sa idon kasashen duniya, ci gaba ne da aka samu. Bugu da kari mai bada taimako kan harkokin tsaron kasar Amurka Susan Rice ta bayyana cewa gwamnatin kasarta na da burin ganin bayan gwamnatin Syria sannu a hankali, amma ba ta da nufin shiga yakin basasar kasar. Har ila yau Amurka ba za ta dauki matakin soja da zai yi kama da na Iraki ko yakin kasar Afghanistan ba.
Sai dai sakamakon wani sabon binciken jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa, ko da yake gwamnatin Amurka na cewa akwai tabbatattun shaidu dake tabbatar da cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula, duk da haka yawancin Amurkawa ba sa goyon bayan daukar matakan soja kan Syria.
A wannan rana, kamfanin watsa labarai na CBS na kasar Amurka, ya bayar da labari game da tattaunawarsa da shugaba Bashar-Al-Assad na Syria, inda shugaba Bashar ya yi gargadin cewa, idan har Amurka na da nufin daukar matakan soja kan kasarsa, to ya dace ta shirya sosai, domin kuwa zata fuskanci ramuwar gayya ta ko wace irin hanya. (Bilkisu)