in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaran wasannin Olympic na Landan a ranar 9 ga wata
2012-08-10 10:23:08 cri

Ya zuwa ranar 9 ga wannan wata, agogon birnin Landan na kasar Birtaniya, an shiga rana ta goma sha uku na gasar wasannin Olympic na shekarar 2012. A wannan rana, gaba daya akwai lambobin zinare da yawansu ya kai 22 da aka lashe a gasar, tawagar kasar Sin ta lashe lambar zinariya guda daya da na azurfa guda biyu, tawagar Amurka ta lashe lambobin zinare guda biyar, kuma yawan lambobin zinare da tawagar kasar Amurka ta samu ya kai 39, hakan ya sa ta kasance a matsayi na farko wajen yawan lambobin zinare da ta samu inda ta sha gaban kasar Sin.

A wasan karshe na tsunduma ruwa daga dandamalin tsayin mita 10 na mata, 'yar kasar Sin Chen Ruolin wadda ta taba lashe lambar zinariya a gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekara ta 2008 ta sake zama zakara a wasan, inda 'yar kasar Austrelia ta lashe lambar azurfa yayin da 'yar kasar Malaysia ta lashe tagulla. Lambar zinariya da Chen Ruolin ta lashe ita ce lambar zinariya ta 200 da kasar Sin ta samu a yayin gasannin wasannin Olympics na yanayin zafi da aka shirya a tarihi.

A wasan karshe na wasan karate na mata na ajin kilogram 57, 'yar wasan kasar Sin Hou Yuzhuo ta lashe lambar azurfa sakamakon kashin da ta sha a karawar da ta yi da 'yar wasan kasar Birtaniya Jones Jade wadda ta lashe lambar zinariya da maki 4 da 6. Ban da wannan kuma, 'yar wasan kasar Faransa Harnois Marlene da 'yar wasan lardin Taibei na kasar Sin sun lashe lambobin tagulla tare.

A wasan karshe na damben boxing na ajin kilogram 51 na mata, 'yar kasar Sin Ren Cancan wadda ita ce zakarar duniya ta lashe lambar azurfa ne sakamakon kashin da ta sha a karawar da ta yi da shahararriyar 'yar wasan damben boxing ta kasar Britaniya Adams Nicola da maki 7 da 16. Adams Nicola ta lashe lambar zinariya a wasan damben boxing na mata ta farko a tarihin gasar wasannin Olympics.

A wannan rana ne, aka kammala gasar kwallon ruwa ta mata, inda kasar Amurka ta lashe lambar zinariya, kana kasar Sin ta samu lamba ta biyar a yayin gasar.

Kazalika, a wasan karshe na gudun mita 200 na maza, 'dan kasar Jamaica Usain Bolt ya lashe lambar zinariya cikin dakika 19 da digo 32, inda ya kasance 'dan wasa daya tilo wanda ya ci gaba da lashe lambar zinariya a gudun mita 100 da na mita 200 har sau biyu a tarihin gasar wasannin Olympics. Ban da wannan kuma, sauran 'yan wasan kasar guda biyu wato Blake Yohan da Weir Warren sun lashe lambobin azurfa da tagulla na wasan.

Ya zuwa ranar 9 ga wannan wata, gaba daya, tawagogi 43 sun samu lambobin zinare, guda 80 sun samu lambobin yabo. Kasashe shida da ke kan gaba a gasar, sun hada da kasar Amurka wadda ta samu lambobin zinare 39, kasar Sin wadda ta samu lambobin zinariya 37, kasar Birtaniya 25, Rasha 12, Korea ta kudu 12, sai Jamus mai lambobi 10.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China