in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaran wasannin Olympic na Landan a ranar 8 ga wata
2012-08-09 10:16:27 cri

Ya zuwa ranar 8 ga wannan wata, agogon birnin Landan na kasar Britaniya, an shiga rana ta goma sha biyu na gasar wasannin Olympic na shekarar 2012. A wannan rana, gaba daya akwai lambobin zinare da yawansu ya kai 17 da aka lashe a gasar, tawagar kasar Sin ta lashe lambobin zinare a wasan kwallon tebur da na karate guda biyu, yawan lambobin zinare da tawagar kasar Sin ta samu ya kai 36, har yanzu tana cigaba da kasancewa a matsayi na farko wajen yawan lambobin zinare da ta samu a gasar wasannin Olympic na Landan.

A wasan karshe na kwallon tebur na maza, kasar Sin ta doke kasar Korea ta kudu da ci uku ba ko daya, inda ta ci gaba da rike kambunta a fagen wasan kwallon tebur a wasannin Olympics, hakan ya sa tawagar kasar Sin ta lashe daukacin lambobin zinare na wasan kwallon tebur a Landan. Kasar Korea ta kudu ta lashe lambar azurfa a wannan gasa, kasar Jamus ta lashe lambar tagulla bayan da ta doke yankin musamman na Hongkong na kasar Sin a gasar.

A wasan karate ta mata na ajin kilogram 49, 'yar wasan kasar Sin Wu Jingyu ta doke 'yar kasar Spaniya Yague Enrique Brigitte inda ta ci gaba da kasancewa zakara a yayin wasannin Olympics, yayin da Yague Enrique Brigitte ta lashe lambar azurfa.

A wasan kokawa ta mata na ajin kilogram 63, 'yar wasan kasar Sin Jing Ruixue ta lashe lambar azurfa yayin da shahararriyar 'yar wasan kasar Japan Icho Kaori ta lashe lambar zinariya.

A wasan damben boxing na mata na kusa da na karshe, 'yar wasan kasar Sin Li Jinzi ta lashe lambar tagulla sakamakon kashin da ta sha a karawar da ta yi da 'yar kasar Rasha Torlopova Nadezda.

Ban da wannan kuma, a gasar neman lashe lambar tagulla a wasan kwallon raga kan rairayi na mata, 'yan wasan kasar Sin Xue Chen da Zhang Xi sun sha kashi a hannun 'yan wasan kasar Brazil, yayin da 'yan wasan Amurka suka lashe lambobin zinare da azufa.

Kazalika, a gasar gudun ketare shinge na mita 110 na maza, 'dan wasan kasar Amurka Merritt Aries ya lashe lambar zinariya yayin da 'dan wasan kasar Sin Liu Xiang ya fita daga gasar sakamakon ciwon kafa, haka kuma, 'dan wasan kasar Cuba Robles Dayron wanda ya taba lashe lambar zinariya a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ma ya fita daga gasar sakamakon raunin da ya ke fama da shi a cinyarsa.

Ya zuwa ranar 8 ga wannan wata, gaba daya, tawagogi 41 sun samu lambobin zinare, guda 76 sun samu lambobin yabo. Kasashe shida da ke kan gaba a gasar, sun hada da kasar Sin wadda ta samu lambobin zinare 36, kasar Amurka ta samu lambobin zinariya 34, kasar Birtaniya 22, Korea ta kudu 12, Rasha 11 sai kuma Faransa mai lambobi 8.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China