Ana fatan gwamnatin Nijeriya ta fara aikin share fage na wasannin Olympics masu zuwa
A ran 11 ga wata, tsohon shugaban kungiyar wasannin tsalle tsalle da guje guje na kasar Nijeriya Mista Toni Urhobo ya bayyana cewa, a wasannin Olympics na London, tawagar 'yan wasan Nijeriya ba ta samu sakamako mai kyau ba, wannan dai an riga an san shi idan aka duba aikin share fage da kasar Nijeriya ta gudanar kafin wasannin. Ya ci gaba da cewa, idan wata kasa tana son samu maki mai kyau, to, tilas ne ta shirya sosai, amma a lokacin da ya ba shawara ga kungiyar wasannin tsalle tsalle da guje guje ta Nijeriya, amma ba ta mai da hankali kadan kan shawararsa ba.
Mista Toni Urhobo ya ci gaba da cewa, ya kamata a samu malamai masu horar da 'yan wasa daga ketare, amma sai su yi aiki a Nijeriya. Ya kamata bangarori daban daban su fara kokari yanzu domin gudanar da aikin share fage na wasannin Olympics masu zuwa. (Danladi)