in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi a karo na 30 a birnin Landan
2012-08-13 09:30:03 cri

A ranar 12 ga wata da dare, an rufe gasar wasannin Olympics ta Landan ta lokacin zafi a karo na 30 da aka shafe kwanaki 16 ana yinta, 'yan wasan sama da dubu 10 da suka fito daga mambobi 204 na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa sun halarci wannan gasar, haka kuma 'yan wasan sun fafata cikin gasanni 26 na Olympics, kuma an ba da lambobin zinariya guda 300, kuma akwai tawagogi 54 sun samu lambobin yabon zinari, kana tawagogi 85 sun samu lambobin yabo, kuma kasashen Amurka, Sin da Birtaniya suna sahon gaba cikin jerin sunayen kasashen da suka samu lambobin yabo mafi yawa. Haka kuma, a gasar wasannin Olympics ta Landan, 'yan wasa mata da suka halarci wasannin sun cimma burin halartar dukkan gasannin Olympics, kuma kasashen Qatar, Saudiyya da Brunei Darussalam sun tura 'yan wasan mata a Landan.

A gun gasar wasannin Olympics da aka yi na wannan karo, tawagar kasar Sin ta samu lambobin yabo na zinariya 38 da lambobin yabo na azurfa 27, kana da iri na tagulla guda 22, wato su suka tashi lambobin yabo 87, kuma ta kasance a matsayi na 2 cikin jerin kasashen da suka samu lambobin yabo na zinari azurfa da tagulla mafi yawa a duniya, kuma yawan lambobin yabon zinariya da Sin ta samu ya fi na gasar wasannin Olympics na Athens wato 32, kuma 'yan wasan kasar Sin sun kafa bajintar duniya 6, kuma sun kafa bajintar wasannin Olympic 6.

Ban da wannan kuma, a ranar 12 ga wata, kwamitin tsakiya da majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun aika da sakon murna ga tawagar wasannin Olympics a karo na 30 ta kasar Sin, inda aka bayyana cewa, ana fatan tawagar wasannin kasar Sin za su tashi tsaye don takaita fasahohin da aka samu, don ci gaba da inganta kwarewarsu da ladabtarwarsu, don ci gaba da raya harkokin wasanni na kasar Sin ta kimiyya, ta yadda za a cimma burin raya zamantakewar al'umma mai wadata, da ba da babbar gudummawa wajen bude wani shafi na raya ra'ayin zaman gurguzu da ke da halayye irin ta musamman ta kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China