in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaran wasannin Olympic na Landan a ranar 7 ga wata
2012-08-08 10:50:55 cri

Ya zuwa ranar 7 ga wannan wata, agogon birnin Landan na kasar Britaniya, an shiga rana ta goma sha daya na gasar wasannin Olympic na shekarar 2012. A wannan rana, gaba daya akwai lambobin zinare da yawansu ya kai 21 da aka lashe a gasar, tawagar kasar Sin ta lashe lambobin zinare a wasan kasada da na kwallon tebur guda uku, yawan lambobin zinare da tawagar kasar Sin ta samu ya kai 34, har yanzu tana cigaba da kasancewa a matsayi na farko wajen yawan lambobin zinare da ta samu a gasar wasannin Olympic na Landan.

Baya ga gasar wasan kasada, har ila 'dan wasan kasar Sin Feng Zhe ya lashe lambar zinariya ta wasan tseren kwale-kwale wato parallel bars na maza, 'yar kasar Sin Deng Linlin ta lashe lambar zinariya ta wasan taka-ka-fadi wato Balance beam na mata, kana wata'yar wasa daban daga kasar Sin ta samu lambar azurfa. Ban da wannan kuma, 'dan wasan kasar Sin Zou Kai ya lashe lambar tagulla ta wasan tseren kwale-kwale wato horizontal bar na maza.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China