in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karyata kai hari a kan motocin Assad
2013-08-09 15:26:30 cri

An kebe ranar 8 zuwa 10 ga wata a matsayin ranakun hutu na karamar Sallar bana a kasar Siriya, kuma a ranar salla, shugaban kasar Bashar al-Assad ya je masallacin Anas bin Malik don yin salla, shugaban majalisar dokoki da manyan malaman addini na kasar sun halarci sallar a wannan rana.

Wani hafsa na bangaren 'yan adawa na kasar Siriya ya bayyana cewa, dakarun dake adawa da gwamnati sun kai hari a kan ayarin motocin shugaban Assad a kan hanyarsa ta zuwa masallacin, kuma an yi lugudan wuta a kan wasu motocin. Game da wannan batu, ministan yada labaran Syria Omran Zoabi ya karyata zargin. Yana mai cewa, shugaba Assad bai shiga ayarin motocin ba, shi ya tuka motar da kansa zuwa masallacin, kuma ya yi hira sosai tare da manyan jami'an gwamnatin da shehunan malamai na addinin Musulunci da suka je Salla a masallacin, kuma ya taya duk al'ummar kasar murnar karamar salla ta bana.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China