Bisa labarin da gidan telebijin na Al-Arabiya da na Al Jazeera suka bayar, an ce, dakarun adawa da gwamnati sun riga sun mamaye sansanin sojojin sama na Minnigh.
A sa'i daya kuma, a ranar 6 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Siriya ya ruwaito daga wata majiya cewa, an musunta labarin cewa, bangaren adawa ya mamaye sansanin Minnigh, inda wannan majiya ta ce, sojojin gwamnatin da ke kewaye da sansanin Minnigh sun fafata yaki da 'yan ta'adda, kuma dukkan ma'aikatan da ke sansanin suna cikin koshin lafiya.
A wata sabuwa kuma, kwanan baya, dakarun da ke adawa da gwamnati sun mamaye garin Alawites da ke lardin Lattakia, kuma sun fara isa kusa da garin shugaba Assad wato al-Khalidieh. Gidan telebijin na Al-Arabiya ya ruwaito bayani daga bangaren adawa cewa, yanzu, dakaru masu adawa da gwamnati suna gwabza fada da sojojin gwamnati a garin Alam da ke arewa da al-Khalidieh. A wannan rana kuma, kamfanin dillancin labaru na Siriya ya ba da labari cewa, sojojin gwamnati sun riga sun maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Alam, kuma sun murkushe 'yan ta'adda da ke wurin.(Bako)