A wannan rana, yayin da Zhou Xiaochuan dake halatar taron koli na kungiyar kasashen G20, ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, aikin kafa gidauniyar hadin gwiwar ajiyar kudaden kasashen waje ta kasashen BRICS, an yi shi ne bisa tushen musayar kudi na kasashen ketare daban daban, kuma an yi koyi ne daga irin tsarin hadin gwiwa ta yin amfani da takardar kudi iri guda a wasu yankuna. Haka kuma, da farko za a samar da kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 100 a gidauniyar, kuma kasar Sin za ta bayar da akasarin kudaden.
Yayin da aka tabo maganar irin tasirin da matakin da kasashe masu wadata suka dauka na daina aiwatar da manufar bude bakin aljihu zai haifar, Zhou Xiaochuan ya ce, kasar Sin na da kwarewa sosai wajen warware wannan batu, kuma a shirye take, tun da aka fara daukar wannan mataki.(Bako)