in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen warware batun tattalin arzikinta
2013-09-05 17:26:03 cri

A ranar 5 ga wata, a birnin Saint-Petersburg da ke kasar Rasha, za a yi taron koli karo na 8 na rukunin kasashen kungiyar G20. A gabanin fara taron, yayin da mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao ke zantawa da manema labaru na gida da waje, ya ce, idan kasar Sin ta iya warware batun tattalin arzikinta, hakan zai zama babbar gudummawar da za ta bayar wajen raya tattalin arzikin duniya.

Fadar Constantin mai tarihin shekaru 300 da ke bakin tekun Neva, wadda kuma ke dab da yankin Gulf na kasar Finland, ta sake jawo hankalin kasashen duniya a matsayinta na wurin taron koli karo na 8, na kungiyar kasashen G20, wannan fada ta bude kofarta don maraba da baki daga kasashen duniya daga ranar 4 ga wata, cikinsu kuwa, har da tawagar kasar Sin wadda ke jawo hankalin kasashen duniya sosai.

Taken taro na wannan karo shi ne "Sa kaimi ga raya tattalin arziki da samar da guraben aikin yi. Gabanin fara taron, yayin da mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao ke zantawa da wakilinmu, ya ce, yanzu, tattalin arzikin kasashen duniya na ci gaba da kasancewa cikin hali na rashin tabbas, don haka shirya taron koli na kungiyar G20, a daidai wannan lokaci na da ma'anar musamman, yana mai cewa,"Bankin ajiyar kudaden kasashen waje na kasar Amurka ya sanar da cewa, zai dakatar da daukar matakan bude bakin aljihu, lamarin da ya haddasa tangal-tangal a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, sannan kuma, ya yi sanadiyyar tangal-tangal a kasuwar kudi ta kasashen da suke samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, har ma a wasu kasashe, ana fuskantar kalubale na janye jarin zuwa kasashen waje, da raguwar darajar kudadensu."

Mr. Zhu ya bayyana cewa, ban da irin wadannan kalubale, kasashen Turai ba su tsallake daga mummunan tasirin da matsalar basussuka ta kawo ba, haka kuma, kasashen da suke samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, su ma suna fuskantar wasu sabbin matsaloli. Game da wadannan batutuwan da ke shafar makomar tattalin arziki na kasashen duniya, kullum kasar Sin na nacewa kan warware batun tattalin arzikin kanta. Mr. Zhu ya ce,"Da farko dai, ya kamata mu warware batun kasar Sin, ciki hadda ci gaba da karfafa aikin yin gyare-gyare game da tsarin tattalin arziki, da kyautata ingancin karuwar tattalin arziki, da fuskantar kalubale a sakamakon daidaita saurin bunkasuwar tattalin arziki, da canja salon raya tattalin azriki, da aka yi a baya, don tabbatar da ci gaba da raya tattalin arziki yadda ya kamata."

Ban da wannan kuma, Zhu Guangyao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki matakai don tinkarar wadannan kalubale, a sa'i daya kuma, kasar Sin tana da cikakken imanin tabbatar da samun karuwar tattalin arziki da yawansa zai kai kashi 7.5 cikin 100 a shekarar 2013, a cewarsa,"Yanzu, ana canja salon raya tattalin arziki bisa manufar kiyaye muhalli da tsimin makamashi, don samun bunkasuwar shi, haka kuma, mun yi imani cewa, za a ci gaba da daidaita tsarin raya tattalin arziki, don ba da tabbaci wajen kyautata ingancin samun karuwar tattalin arziki. A sa'i daya kuma, mu kayyade yawan hauhawar farashin kayayyaki da ya yi kasa da kashi 3.5 cikin 100, tare da cimma burin samar da guraben aikin yi, da yawansu zai kai sama da miliyan 10. Za mu yi kokarin kawo alheri ga jama'ar kasarmu, a sa'i daya kuma, kasashen duniya za su ci moriya daga bunkasuwar tattalin arzikin namu."

Ban da wannan kuma, Zhu Guangyao ya ci gaba da bayyana cewa, kasar Sin za ta mayar da tsarin yin shawarwari na kungiyar kasashen G20, don ya zama wani muhimmin dandali na daidaita batun samun bunkasuwar gamayyar tattalin arziki ta kasashe masu wadata da kasashen da suke samun saurin bunkasuwar tattalin arziki.

Har wa yau, a gun taron koli na wannan karo, tawagar kasar Sin ta kafa wata cibiyar yada labaru dake da fadar da ta kai muraba'in mita sama da 400, don samar da labarun da suka shafi tawagar kasar Sin a yayin taron koli na kungiyar ta G20, da bayyana wa kasashen duniya matsayin da kasar Sin ke kai game da manyan batutuwan duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China