in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun raya tattalin arziki shi ne abin da za a mai da hankali sosai a gun taron koli na G20
2013-09-03 17:38:06 cri

Daga ranar 5 zuwa 6 ga wata, a birnin St Petersburg da ke kasar Rasha, za a gudanar da taron koli na rukunin kasashen G20. Kasar Rasha da ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar G20 na wannan zagaye, ta bayyana cewa, taron zai tantance ayyukan da rukunin kasashen G20 ya yi cikin 'yan shekarun nan, tare da bayar da wani rahoto. A daya hannu kuma, ba za a tattauna batun kasar Siriya a hukunce ba a gun taron wato da ma, taro ne da ke tattauna batun tattalin arziki kawai.

Taron koli na G20 da za a yi a birnin St Petersburg da ke kasar Rasha, ya kasance taron kolin kungiyar karo na 8, tun bayan da aka kafa kungiyar, haka kuma, ya kasance karo na farko da kasar Rasha ta dauki nauyin shirya taron a matsayin kasar da ke shugabantar G20. Yayin da wakilin kasar Rasha a kungiyar G20 kuma mataimakin ministan kudi na Rasha Sergey Storchak ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, don cimma burin taron, kasar Rasha ta tsara wasu ka'idoji game da taron koli da kuma harkokin da za a gudanar a yayin taron, ya ce, "Da farko dai, za a mai da hankali game da samun karuwar tattalin arziki. Na biyu kuma shi ne, a dora muhimmanci kan bunkasa dangantakar abokantaka da kasashen duniya, wato bai kamata kungiyar kasashen G20 ta rufe kofarta, ya kamata su yi amfani da wannan dandanlin hadin gwiwa don karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe. Na uku shi ne, a mai da hankali game da batun da ya shafi duniya da na shiyya-shiyya, kuma abin da ke gaban kome shi ne batun samar da isashen abinci.

Game da nasarorin da ake fata za a cimma a gun taron koli na wannan karo da aka dora mihimmanci sosai a kai, mai kula da kasashen G20 na kasar Rasha kuma shugabar ofishin kwararru na shugaban kasar Rasha, Ksenya Yudaeva ta fada wa wakilinmu cewa, shugabanni mahalartar taron za su daddale yarjejeniyoyi da dama, ta ce, "Za a daddale wasu yarjejeniyoyin da ke shafar tabbatar da samun karuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci da kuma dorewa, da sa kaimi ga samar da guraben aikin yi, da musayar bayanai game da yaki da masu gudun biyan haraji."

A dayan hannu kuma, za a mai da hankali game da manufofin kudi na kasashen kungiyar, da yadda suke samar da guraben aikin yi, kuma ana fatan kasashen duniya za su cimma daidaito don inganta hadin gwiwa tsakaninsu game da wadannan batutuwa. Yudaeva ta ce,"Ma'aikatun kudi na kasashen ne ke gudanar da manufofin kudi bisa tsare-tsare nasu. A ganina, za a cimma daidaito tsakanin burin raya tattalin arziki cikin gajeran lokaci, da tsara manufar kudi cikin matsaikatan lokaci. A sa'i daya kuma, game da aikin yin gyare-gyare kan tsarin saka jari, ya kamata wasu kasashe su dauki nauyin da ke wuyansu."

Ban da wannan kuma, Yudaeva ta gaya wa wakilinmu cewa, a matsayin wani dandalin dake tattauna batun tattalin arziki, a gun taron koli na G20, ba za a tattauna batun kasar Siriya a hukunce da ke daukar hankalin kasashen duniya ba, tana mai cewa,"Ba shakka, za a tattauna batun Siriya a gun shawarwari na bangarorin biyu, amma ya zuwa yanzu, ba a samu shawarwarin da ke shafar mayar da wannan batu cikin taken taron ba. Haka kuma, na fahimta cewa, batun kasar Siriya ya kasance wani batu mai muhimmanci da yanzu ake tattaunawa sosai. Amma, muna da wasu batutuwan da suke da muhimmanci kamar batun kasar Siriya.

Ban da batun kudi, da samar da guraben aikin yi, da harkokin makamashi, da cinikayya, haka kuma, za a bayar da wani rahoto game da aikin da kungiyar G20 ta yi a cikin 'yan shekarun nan.

Yudaeva ta bayyana cewa, kasar Rasha ce ta dauki nauyin rubuta wannan rahoto, kuma abubuwan da ke kunshe a ciki, sun hada da ayyukan da G20 ta sanya a gabanta, ciki har da aikin sa kaimi ga samar da muhimman abubuwan more rayuwa, da samar da guraben aikin yi, da samar da isasshen abinci, da batun raya tattalin arziki cikin dorewa, da sa kaimi kan yadda mutum shi kansa da zai saka jari.

A hakika dai, kasar Rasha da ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar G20 karo na farko, ta dora muhimmanci sosai game da ayyukan da za a yi a karkashin tsari na G20.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China