Wanda aka tsaida a tsawon kwanaki biyu, zaben na sojojin kasar zai gudana a cikin jihohin kasar Senegal da dama. A yayin zaben shugaban kasar zagayen farko, ba'a samu halartar kada kuri'u ba daga sojojin kasar. A ranar 25 ga watan Maris, fiye da 'yan kasar Senegal miliyan biyar ne ake sanya ran za su kada kuri'u a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.
Shugaban kasar mai barin gado, Malam Abdoulaye Wade na sake neman wani wa'adi na uku a gaban tsohon faraministan kasar Macky Sall wanda ya samu nasarar zuwa na biyu a zaben shugaban kasar zagayen farko.(Maman Ada)