in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya hana Wayne Rooney zama dan wasa mafi kwarewa?
2013-09-06 14:05:30 cri

Ga misali a ranar 19 ga watan Oktobar shekarar 2002, Wayne Rooney ya fara yin suna sakamakon kokarin da ya yi na nuna bajimta, yayin gasar da kungiyarsa ta Everton ta buga da kungiyar Arsenal, wadda a lokcin ke kare kambinta, inda Rooney ya tallafa wajen kawo karshen tarihin kungiyar ta Arsenal, wato na kasancewarta zakara a wasanni 30 da ta lashe a jere.

Shekaru 2 bayan hakan kuma, wato a shekarar 2004, Rooney wanda a lokacin shekarunsa ba su kai 19 ba, ya sake samun wata daukaka, inda ya jefa kwallaye 4 a gasar cin kofin zakarun Turai. Sa'an nan, a farko farkon komawarsa zuwa kungiyar Manchester United, ya taimaka matuka wajen lallasa Asenal da ci 2 da nema, a wannan lokaci Rooney ya jefa kwallo 1 a raga, ya kuma taimakawa wajen samun nasarar jefa kwallo ta Biyu, lamarin da ya sanya Arsenal fadowa a teburin wasannin gasar Premier League ta wannan lokaci, bayan ta samu nasara a wasanni 49 da ta buga.

A sabili da kwarewar da Rooney ya nuna a matsayinsa na dan wasa matashi, ya sa jama'a ke jinjina masa kwarai. Ga misali, kocin Manchester United Sir Alex Ferguson shi da kansa, a lokacin ya yabawa Rooney, yana mai cewa ya kasance dan wasa matashi mafi kwarewa a Ingila a cikin shekararu 30 da suka gabata. Irin yabon da ya sanya Rooney ya fara kallon kansa a matsayin tauraro mafi muhimmanci a fagen gasar Premier League, lamarin da ya sanya shi fara kokarin neman karin albashi, har ma ya taba barazanar cewa zai bar kungiyar Manchester United idan har bukatarsa ba ta biya ba.

Amma abin tambaya a nan shi ne, shin ko a hakika yabon da aka yi wa Rooney ya dace da kwarewar da ya samu? Mun san cewa, fasahohin buga kwallon suna da yawa, kuma su kan sha bamban da juna, bisa yankunan duniya daban daban.

Alal misali, kulaflikan kasar Spain sun fi mai da hankali kan kwarewar 'yan wasa, yayin da kungiyoyin kasar Italiya ke dora muhimmanci matuka kan dabarar kungiya ta kashin kanta. Kana a kasar Birtaniya kuma, an fi mai da hankali kan kokarin hadin kan 'yan wasa, da mika kwallo da karfin jiki, inda ake bukatar 'yan wasa su yi gudu da sauri, da kokarin kwatar kwallo daga abokan karawa. Saboda haka, ana samun 'yan wasa masu karfin jiki, wadanda ke iya gudu da sauri da yawa a kulaflikan kasar Ingila, amma kalilan ne daga cikinsu ke iya sarrafa kwallo da kyau, bisa cikakkiyar kwarewa.

Hakan ne ma ya sa Wayne Rooney, da ya yi fice a wannan fage na sarrafa kwallo ya samu damar samun karin daukaka. Wani dalilim ma shi ne, yadda kafofin yada labaru na kasar Birtaniya, wadanda ke da tasiri sosai a duniya, suka yi ta yayata kwazon Rooney, da fatan hakan zai sanya shi zama abin yabo a fannin wasannin motsa jiki, lamarin da a iya cewa yayi tasiri matuka. Amma a hakika, duk da cewa Rooney ya kasance wani zakakuri a Birtaniya, ba saifai ya kan samu damar nuna kwarewa sosai a manyan gasannin kasa da kasa ba.

Wato dai Rooney ya zamto ginshiki a kungiyarsa ta gida Ingila, amma bai kasance a matakin farko, a kungiyar Manchester United da yake takawa leda. Bisa hakan wasu ke ganin da Rooney ba haifaffen Ingila ba ne, to da kuwa bai samu damar zama Daya daga 'yan wasa mafiya muhimmanci a kungiyar Manchester ba.(Bello Wang/Saminu Alhassan Usman)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China