in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya hana Wayne Rooney zama dan wasa mafi kwarewa?
2013-09-06 14:05:30 cri

Sai dai zuwa kakar wasanni ta shekarar 2010 zuwa ta 2012, Rooney ya sake samun wani rauni mai tsanani, a karawarsu da kungiyar kasar Jamus a gasar cin kofin duniya. Bayan komawarsa Manchester United, kocin kulaf din Sir Alex Ferguson ya fara mai da shi dan wasan tsakiya, wanda ke raba kwallo ga 'yan gaba.

Ya zuwa shekarar 2012, bayan da Robinvan Persie da Shinji Kagawa suka shiga jerin 'yan wasan kungiyar ta Manchester United, Rooney ya sake fadawa cikin wani mawuyacin hali, ganin yadda Robinvan Persie ya fi shi nuna kwazo wajen sarrafa kwallo a gaba, kana Shinji a nasa bangare ya fi Rooney a fagen mika kwallo. Har ila yau karfin jikinsa bai dawo kamar yadda yake a da ba, don haka ya gaza taka kwallo a matsayin dan wasan gaba mai 'yanci. A takaice dai duk da kasancewarsa dan wasa da ya iya buga sassan daban daban, a hannu guda ya kasa zama zabi na farko a dukkanin sashen da yake bugawa ga mai horar da 'yan wasa.

Wayne Rooney ya shiga kungiyar Manchester United ne a lokacin da taurarin kungiyar ke cikin wani yanayi na koma baya, kana Ruud van Nistelrooy wanda ya fi taka rawar gani a cikin 'yan gaban kungiyar, shi kansa bai kai ga matakin farko a fannin gudu ba. Don haka, sauri, da gudun Rooney ya burge jama'a sosai a lokacin.

Duk da cewa, Rooney bai kai Michel Owen da Ronaldo ta fuskar gudu ba, a hannu guda masu kallon wasansa zasu tabbatar da cewa, shi ma dan wasa ne da kan iya yin matsin lamba sosai ga 'yan bayan kowace kungiyar kwallo da ya hadu da ita. Sai dai duk da kwazon da ya rika nunawa a farko farko, raunin da ya ji a watan Afrilu na shekarar 2010, ya lalata yanayin da yake ciki matuka, inda ya rasa karfin jiki da kuzarin da aka san shi da shi a baya.

Kuma wani abin lura ma shi ne, a mafi yawan lokaci Rooney kan yi kokarin fafatawa da 'yan bayan kungiyar da suke buga wasa da su ne, ta hanyar amfani da karfin jikinsa a maimakon fasaha. Hakika Rooney na da karfi da nauyi, wanda hakan ne ma ya sa ake yi masa lakabi da kalmar 'kakkarfa'.

A lokuta da yawa yayin da wannan dan wasa ke kokarin kwatar kwallo a tsakanin 'yan wasa, ko kokarin ratsa 'yan bayan wata kungiya, yana gudu ne tamkar wata motar yaki, wadda ba wanda ke iya yi mata birki. Amma sakamakon yadda ya rika samun raunuka, tare da nauyin jiki, sannu a hankali ya fara rasa kwarewarsa wajen ratsa 'yan baya. Bugu da kari rauni da ya ji a shekarar 2006, ya sanya shi dari-dari wajen yin motsi da karfi, ko shiga rintsin 'yan wasa, kana zuwa shekarar 2010, ya zama mawuyaci ne gare shi ya iya tserewa wani dan wasa dake binsa a guje, yayin da yake kokarin sarrafa kwallo.

Idan kuma muka koma fannin yawan cin kwallaye, Rooney bai zamo kan gaba tsakanin takwarorinsa ba. Duk da cewa, har zuwa yanzu, yana da dabarun kwatar kwallo a cikin da'irar bugun daga kai sai mai tsaron gida, gami da fasahar jefa kwallo a raga. Sai dai a iya cewa, bai kasance cikin sahun fari a wannan fage ba.

Duk da cewa, ana ganin Wayne Rooney a matsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasan gaba na kasa da kasa, amma a kashin gaskiya ya gaza zama cikakken gwani a fannin cin kwallo, musamman idan an kwatanta shi da ragowar zakaru, da duniya ke tinkaho da su a gasar cin kofin zakarun Turai.

Manazarta harkokin wasan kwallon kafa da dama sun fadi albarkacin bakinsu kan dalilin da ya sa Wayne Rooney ya kasa zama dan wasan mafi kwarewa a duniya, inda wasu ke ganin hakan ba ya rasa nasaba da kasancewarsa haifaffen kasar Ingila, matakin da ya sanya shi shan yabo daga mutanensa, da kulaf din da yake bugawa wasa, dama dubban 'yan kallo da ke kewaye da shi.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China