An dai kai ruwa rana a zango na 4 na wasan, kafin Angolan ta samu wannan nasara. Da wannan nasara da Angolan ta samu ta zamo a matsayi na farko, cikin jerin kasashen da suka shiga gasar, sai kuma Masar dake biye mata, inda kuma kasar Tunusiya ta zamo ta uku, sai kuma Madagaska dake matsayi na Hudu.
An dai fara wannan gasa ajin matasa 'yan kasa da shekaru 16 ne a ranar 28 ga watan Yunin da ya gabata, inda kasashe 10 da suka hada da Madagaska, da Tunusiya, da Cote d'Ivoire da Algeriya suka fara fafatawa. Ragowar kasashen da suka shiga gasar sun hada da Gabon, da Masar, da Angola, da Mozambique, Kamaru da kuma dimokaradiyyar Congo.
Wannan dai dama da Angola ta samu ya ba ta zarafin shiga gasar kwallon Kwando ta duniya, wadda zata gudana a birnin Dubai a shekarar badi. Wannan ne kuma karo na Uku da kasar Madagaska ta dauki bakuncin manyan gasanni, bayanda ta dauki bakuncin makamanciyar wannan gasa ta mata a shekarar 2009, da kuma ta ajin maza a shekarar 2012.