in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AL sun bukaci kasashen duniya da su hana amfani da makamai masu guba
2013-09-02 16:15:50 cri


An kira taron ministocin harkokin wajen kungiyar kawancen kasashen Larabawa wato AL karo na 140 a jiya Lahadi 1 ga wata a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar. A cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, an sake nanata cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar Syria ta dauki alhakin harin da aka kai da makamai masu guba a kasar, an kuma yi kira ga MDD da kasashen duniya da su dauki nauyin dake kansu bisa dokokin kasashen duniya, domin daukar matakan hana amfani da makamai masu guba a kasar.

A cikin jawabin da ya yi a yayin taron, ministan harkokin wajen kasar Masar, Nabil Fahmy yana mai cewa, gwamnatin kasar Syria ba ta iya tattaunawa da daukar matakan da suka dace ba don biyan bukatun jama'a, a maimakon haka sai ta dauki matakin soja. Saboda haka, kamata ya yi ta dauki alhakin jama'ar kasar. Amma a sa'i daya Fahmy ya jaddada cewa, a ganin kasar Masar, hanyar siyasa ita ce hanya daya kacal wajen warware matsalar Syria, tana kuma adawa da tsoma baki ta hanyar daukar matakan soja da kasashen ketare za su yi kan kasar.

"Kasar Masar na adawa da duk wani irin nau'in tsoma baki ta hanyar matakan soja daga kasashen ketare, wannan ba wai Masar tana kiyaye wani mulkin da bai biyan bukatun jama'arsa ba, sai dai domin matsayin da Masar ke dauka wajen bin tsarin dokoki na MDD. Na sake nanatawa a nan cewa, hanya daya kacal wajen farfado da zaman karko a Syria ita ce, gwamnatin kasar da masu adawa su halarci taron Geneva karo na biyu da kasashen duniya za su shirya, da kuma amince wa da kafa mulkin wucin gadi da tabbatar da sahihin tsarin dimokuradiyya a kasar."

Fahmy ya kuma bayyana cewa, yanzu shekara uku ke nan da tayar da rikicin kasar Syria, Syria ta kasance cikin yankin da ake fama da yaki inda rukunoni daban daban na kasar da na kasashen ketare ke fafatawa da ita, dalilin da ya sa take fuskantar hadarin samun baraka, wannan zai kawo barazana ga samun zaman karko na nahiyar.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Saudiya, Saud Al Faisal ya ba da tabbacin kai hari kan fararen hula ta hanyar amfani da makamai masu guba da gwamnatin kasar Syria ta yi, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kutsa kai don hana gwamnatin Assad wajen kara amfani da makaman kare dangi.

"Gwamnatin Syria ta riga ta keta layukan da aka shata. Da farko, ta yi amfani da makamai na yau da kullum, yayin da ta gano cewa babu wanda ya hana ta, sai ta yi amfani da makamai masu guba. Mu da jama'ar Syria muna bukatar kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace don hana aikata miyagun ayyukan kashe fararen hula da gwamnatin kasar ke yi."

Shugaban gamayyar kungiyoyin 'yan adawar kasar Syria wato NCSRO F, Ahmad Jarba, wanda ya wakilci kasar Syria don halartar taron ministocin harkokin wajen, shi ma ya bukaci kasashen Larabawa da su nuna goyon bayan daukar matakin soja kan gwamnatin Syria, sa'a nan ya zargi kasashen ketare da tsoma baki kan harkokin Syria.

"Jama'ar kasar Syria ba za su yi hakuri kan mulkin Assad ba, wanda ya murkushe jama'arsa, tauye mulkin kansu, wulakanta akidansu, take mutuncinsu, tare kuma da nufin halaka kasar Syria. An aikata wadannan abubuwa ne tsakanin Damascus da Tehran."

A yayin taron kuma, babban sakataren kungiyar AL Nabil Elaraby ya jaddada cewa, dole ne a hanzartar daddale wani shirin warware rikicin Syria a siyasance, don cimma burin mulkin kasa yadda ya kamata. A sa'i daya kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, don tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin bangarori daban daban na Syria.

"Na sake nanatawa a nan ne cewa, dole ne mu dauki matakan jin kai na gaggawa, ciki har da shirya taron gaggawa na kwamitin sulhu, tsaida wani kudurin da ya zama wajibi, bukaci bangarori daban daban don tabbatar da tsagaita bude wuta a dukkan fannoni, tsara wani tsarin zartaswa da ya dace, da kuma bude wata hanyar ceton jin kai. Matakan da za su iya samar da muhalli mai kyau wajen shirya taron Geneva karo na biyu game da batun Syria cikin hanzari, tare kuma da bude hanya mai kyau wajen daddale shirin warware matsalar a siyasance."

An shirya taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AL a ranar 1 ga wata wanda da ma aka shirya a ranar 3 ga wata sakamakon sabon yanayin da ake ciki a Syria. Taron na wannan karo ya kasance na karshe a cikin wa'adin kasar Masar na shugabantar kungiyar AL. A yayin taron kuma, kasar Libya ta maye gurbinta don shugabantar kungiyar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China