in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sham ta ce zata mai da martani kan hare-hare daga kasashen waje
2013-08-30 15:59:43 cri
A ranar Alhamis 29 ga wata, ministan tsaron kasar Sham, kana mataimakin babban kwamandan sojan kasar, Fahed al- Fraij ya bayyana cewa, sojoji da kuma jama'ar kasar za su tsaya tsayin daka kan mai da martani ga hare haren da wasu manyan kasashen duniya za su kai musu.

A wannan rana, kamfanin dillancin labaran kasar ya ba da labarin cewa, Fahed al- Fraij ya fadi haka ne lokacin da ya buga waya ga takwaransa na kasar Farisa, Hasan Dahqan.

A cikin hirarsu kuma, Hasan Dahqan ya jaddada cewa, dole ne a daidaita batun Sham a siyasance kuma cikin lumana. Ya kara da cewa, wadanda za su tayar da yake-yake, su ne za su ci hasara. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China