in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Obama ya ce ba a tsaida matsaya ta karshe don gane da batun kasar Sham ba
2013-08-31 16:34:37 cri
Rahotanni daga fadar gwamnatin Amurka na cewa, har yanzu ba a tsaida matsaya ta karshe don gane da matakin da za a dauka kan kasar Sham ba.

Da yake tsokaci kan wannan batu jiya Jumma'a a fadar White House, shugaba Barack Obama na Amurka, ya ce yana duba yuwuwar daukar wasu matsakaitan matakai, sakamakon zargin da ake yi na yin amfani da makamai masu guba kan fararen hula a kasar ta Sham.

Obama yace a yanzu haka, baya tunanin amfani da sojojin kasa wajen kaiwa kasar ta Shma hare.

Kafin wannan dai tsokaci wani rahoto ma da fadar gwamnatin Amurkan ta fitar, ya bayyana cikakkun hujjoji da ake ganin na nuna cewa tabbas mahukuntan kasar ta Sham sun yi amfani da makamai masu guba, wajen kaiwa wasu fafaren hula dake zaune a wajen birnin Damascus hare hare, ciki hadda harin ran 21 ga watan Agustan nan.

Fadar gwamnatin Amurka dai ta dage cewa wajibi ne a rataya alhakin wannan ta'asa da ta sabawa dokokin kasa da kasa a wuyan gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad.

A yanzu haka dai shugaba Obama ya yi alkawarin tattaunawa da 'yan majalissar dokokin Amurkan, biyowa bayan bukatar da wasu daga cikinsu suka yi, na neman amincewar majalissar, kafin daukar ko wane irin mataki a kan kasar ta Sham. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China