A makon da ya gabata, Brahimi ya bayyana wa 'yan jarida cewa, bisa shirin da aka tsara, watakila za a gudanar da taron Geneva karo na 2 game da batun Syria a watan Satumba. Wakilan kasashen Amurka da Rasha za su yi shawarwari a birnin Hague a ranar 28 ga watan Agusta, kuma Brahimi da wakilan kasashen biyu za su yi shawarwari a ranar 29 ga wata. Amma a ranar 27 ga wata, kasar Amurka ta sanar da soke ganawar da za a yi a tsakaninta da kasar Rasha.
Madam Mattar ta tabbatar a gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Geneva a wannan rana cewa, kasar Amurka ce ta gabatar da kudurin soke ganawar a birnin Hague.
Kana Mattar ta jaddada cewa, a ganin Brahimi, tsanantar halin rikici a kasar Syria ya bayyana cewa, amfani da karfin tuwo zai kara kawo illa ga fararen hula a kasar, kuma hanyar siyasa ita ce hanya daya kawai ce wajen warware batun. (Zainab)