A halin yanzu dai, ana gudanar da ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa yadda ya kamata, kuma bisa rahoton da aka samu, babu wanda ya rasu ko kuma ya bace sakamakon bala'in a yankunan.
Shugaban hukumar kula da harkokin girgizar kasa ta jihar Tibet ya bayyana cewa, girgizar kasa da ta auku a wannan karo a yankin Changdu girgizar kasa ce mafi muni tun bayan shekaru 10 da suka gabata.
Hukumar kula da harkokin jama'ar jihar Tibet ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an riga an aika da kayayyakin agaji da suka hada da tantuna guda 1200, abinci ton 30, manyan barguna na zamani guda dubu 20, ruwan sha kwalba dubu 4, da kuma abincin dabbobi ton 110 zuwa yankunan da bala'in ya shafa. Bugu da kari, wasu kungiyoyin ba da agaji da kuma na ba da jinya sun riga sun isa yankunan don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. (Maryam)