Awoyi guda 36 bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 6.6 a gundumar Min da gundumar Zhang da ke lardin Gansu, wato ya zuwa daren ranar 23 ga wata, an gano mutane guda 14 wadanda suka bace bayan girgizar kasar, kuma dukkansu sun rasu. Ya zuwa yanzu, mutane guda 95 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar bala'in, yayin da sama da dubu guda sun jikkata.
Har zuwa yanzu dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan jinya. Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin jama'a ta lardin Gansu Zhang Kebing ya bayyana cewa, ana ci gaba da samar da kayayyakin jiyya a wurare da wannan bala'in ya shafa, ta yadda za a tabbatar da ci gaban gudanuwar harkokin yau da kullum ga wadanda abin ya shafa. (Maryam)