in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna juyayi ga wadanda suka rasu cikin girgizar kasar lardin Gansu
2013-07-23 16:16:55 cri
Ran 22 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa da ta auku a garin Dingxi da ke lardin Gansu, tare da nuna fatan cewa, jama'ar kasar Sin za su iya cimma nasarar shawo bala'in da girgizar kasa ta haifar cikin sauri.

Da misalin karfe 7 da minti 45 na safiyar ranar Litinin 22 ga wata nan ne, wata girgizar kasa mai karfin maki 6.6 kan ma'aunin ta auku a yankin iyakar gundumar Min, da gundumar Zhang da ke lardin Gansu. Bala'in ya kawo illa ga gundumomi guda 22, garurruwa guda 204 da kuma mazaunan wurin dubu 123 da ke birane guda 6. Ya zuwa yanzu, mutane 94 ne suka rasu a sanadiyyar bala'in, yayin da kuma guda 1 ya bace, kana 1001 suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China