Kafin taron, wasu mambobin kungiyar sun ba da shawara ga kungiyar EU da ta dakatar da shirin samar da kudin agaji da yawansu ya kai kudin Euro biliyan 5 ga kasar Masar da aka amince da shi a watan Nuwanba na bara, amma ganin yanayin tattalin arziki da ake ciki a kasar da damuwa da aka nuna game da zaman rayuwar jama'a a wurin, a karshe dai, ba a sauya wannan shiri a gun taron ba. Sai dai, an bukaci babbar jami'ar kula da harkokin diplomasiyya da tsaro na kungiyar EU Catherine Ashton da kwamitin kungiyar EU da su sake yin nazari game da samar da kudin agaji ga Masar.
Ban da wannan kuma, kungiyar EU ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankali da ya ci gaba da tsananta a kasar Masar, da aika-aikar ta'addanci a kasar. Haka kuma, shirin kungiyar EU ya bukaci bangarorin daban daban na kasar da su dakatar da rikici, da yin hakuri, a sa'i daya kuma, ya bukaci bangarorin siyasa daban daban na kasar da su bi umurnin jama'a, don yin shawarwari ta hanyar siyasa.
A ranar 21 ga wata, a birnin Alkahira hedkwatar kasar Masar, mataimakin sakatare janar na M.D.D. Jeffrey Feldman ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Nabil Fahmy da sakataren janar na kungiyar hadin gwiwa kan kasashen Larabawa AL Nabil el-Araby, don tattauna yanayin tangal-tangal a kasar Masar.(Bako)