Jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta ruwaito kakakin ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Abdel-Fattah Osman yana cewa, yayin da aka cafke shi, Badie yana boye ne a wani gini na garin Nasr da ke arewa maso gabashin birnin Alkahira.
A ranar Laraba da ta gabata, rundunar tsaro ta kasar Masar ta dauki matakin korar masu goyon bayan Mohamed Morsi a wuraren da ke kusa da masallacin Rabaa El-Adaweya da ke garin Nasr, don kawo karshen zaman dirshan da suka yi har na tsawo makwanni 6.
Kamfanin dillancin labaru na Reutes ya kuma ba da labarin cewa, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Masar ta bayyana cewa, rundunar tsaro ta gudanar da aikin cafke Badie ne, bayan da masu gabatar da kara na kasar suka amince da hakan.
A hakika dai, a karshen watan Yuli na bana, masu gabatar da kara ta kasar sun zargi Badie da sauran manyan jami'ai biyu na kungiyar 'yan uwan Musulmi da zuga tashe-tashen hankali, da bukatar yanke musu hukunci. A watan Agusta kuma, an bayar da labari cewa, za a yanke wa Badie da mataimakansa hukunci a ranar 25 ga wannan wata. Amma ganin rashin cafke Badie a wancan lokaci, manazarta sun bayyana cewa, kila ma, Badie zai bar hukuncin da za a yi masa. (Bako)