in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta goyi bayan binciken da MDD ke gudanarwa a Syria
2013-08-26 20:35:04 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya fada a ranar Litinin cewa, kasar Sin ta goyi bayan matakin da MDD ta dauka na gudanar da bincike game da rahoton da aka samu na amfani da makamai masu guba a kasar Syria.

Wang ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin wakilin kamfanin dillancin labari na Xinhua game da halin da ake ciki a kasar ta Syria da yaki ya wargaza, inda ya ce kasar Sin na daukar batun rahoton da aka samu na amfani da makamai masu guba a Syria da muhimmancin gaske.

Ya ce, matsayin Sin shi ne, ba ta amince da koma wane ne ya yi amfani da makamai masu guba ba. Mr Wang, ya ce kasar Sin tana goyon bayan matakin da MDD ta dauka na gudanar da bincike mai zaman kansa cikin gaskiya da adalci kamar yadda kudurorin MDD suka tanada don gano gaskiyar lamarin cikin hanzari.

Ya ce matakin siyasa ita ce hanya daya tilo na warware batun na Syria, kana abu mafi muhimmanci shi ne a gudanar da zagaye na biyu na taron Geneva game da kasar Syria nan ba da dadewa ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China