in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EU ta yi alkawarin sake ba da kudin agaji da yawansa ya kai kudin Euro miliyan 400 ga Siriya
2013-06-07 16:27:13 cri
A ranar 6 ga wata ne, shugaban hukumar kungiyar EU Manuel Durão Barroso ya sanar da cewa, sabo da yadda yanayin da ake ciki a kasar Siriya ke ci gaba da tabarbarewa, kungiyar EU ta yanke shawarar ci gaba da samar da kudin agaji da yawansa ya kai Euro miliyan 400, domin taimakawa 'yan gudun hijira na Siriya da ke cikin kasar da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. Barroso ya ce, Samar da kudin agajin ba zai warware rikicin Siriya ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne a lalubo bakin zaren warware batun ta hanyar siyasa don kawo karshen rikicin siyasa a kasar.

Ban da wannan kuma, a ranar 6 ga wata, kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka Jen Psaki ta ce, Amurka za ta yi bincike sosai game da rahoton nazari da Faransa ta gabatar cewa, Gwamnatin Siriya na yin amfani da makamai masu guba.

A ranar 4 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya ba da sanarwa cewa, Faransa ta ba da tabbaci cewa, an yi amfani da sinadarin Sari mai guba a wurare da dama a kasar Siriya, amma, a cikin sanarwar, ba a ambaci wane bangare ne ya yi amfani da sinadarin sari na mai guba a kasar ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China