Kuma rahoton ya yi bincike da kuma tantancewa game da batun kare hakkin dan Adam a kasar Siriya daga ranar 15 ga watan Janairu zuwa ranar 15 ga watan Mayu. A cikin rahoton, an ce, gwamnatin Siriya na mallakar makamai masu guba, kuma dakaru masu adawa da gwamnatin su ma, kila sun samu kuma sun yi amfani da makamai masu guba. Sabo da haka, masana sun yi imanin cewa, daga watan Maris zuwa Watan Afrilu, an yi amfani da makamai masu guba cikin rikicin Siriya, amma sai a samu cikakkiyar shaida daga wurin rikicin kawai, za a iya yanke magana a karshe.(Bako)