in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron kwamitin tsaron kasar ta Amurka kan batun Syria
2013-08-25 17:13:00 cri
Ran 24 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kira taron kwamitin tsaron kasar don gudanar da bincike kan sabon labarin dake nuna cewa an yi amfani da makamai masu guba a kasar Syria domin gabatar da matakan da kasar Amurka za ta dauka game da wannna batu.

Cikin sanarwar da gwamnatin Amurka ta bayar, an ce, an yi tattaunawa kan wani rahoto na ranar 21 ga wata cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba a wata karkarar birnin Damascus. Haka kuma shugaba Obama ya saurara matakan da kasar Amurka da gamayyar kasa da kasa za su dauka domin fuskantar wannan matsala.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bisa labaran da aka samu masu tushe da kuma bayani kan halin mutanen da suka rasu a sanadiyyar makaman, yanzu, hukumar leken asiri na Amurka na tattaunawa tare da gamayyar kasa da kasa don ci gaba da tattara labaran dake hakikance gaskiya wannan batu.

Ran 21 ga wata, jam'iyyar adawa ta kasar Syria ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kai farmaki kan wani yankin birnin Damascus da makamai masu guba na "Sarin", wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama, amma sai dai gwamnatin Siriya ta karyata wannan zargi.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya taba nuna cewa, kasar Amurka ba za ta yi hakuri ba idan gwamnatin kasar Syria ta yi amfani da makamai masu guba, kuma a halin yanzu, gwamnatin Amurka na samun matsa lamba daga 'yan kasar domin daukar matakan soja kan batun Syria. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China