A cikin wata sanarwa, Amos ta ci gaba da cewa kasawa a bangaren masu fadace fadacen, na samar da kariya ga jama'a farar hula a fadin kasar ta Syria, ya nuna cewa ana ci gaba da kashe mata, maza da kuma yara kanana, kana ana raunata su, ga kuma rasa muhallinsu a fadin kasar.
Ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su daina aikata dukkan abin da ke haddasa mutuwar farar hula, domin kungiyoyin ba da agaji su isa wajensu, kana su kiyaye dokokin kare 'yancin bil adama karkashin dokar kasa da kasa, inda ta ci gaba da cewa ita da abokan aikinta a fuskar tallafawa bil adama da kiyaye 'yancin bil adama sun sha yin kira da kuma baiyana bukatar dakatar da wannan fada.
Amos ta lura da cewa daruruwan jama'a sun rasa rayukansu, wasu sun samu rauni, kana an yi garkuwa da wasu a hare hare a Homs, Allepo da ma sauran biranen kasar Syria a kwanaki biyu da suka wuce.
Ta ce suna matukar bukatar goyon baya domin su sami isa ga jama'a mabukata a duk inda suke a cikin kasar Syria, tare da karin cewa aikinsu babu nuna goyon baya ko wariya, kuma yana da muhimmanci a tabbatar da cewa kokarin ba da tallafin bil adama ba shi da nasaba da manufa ta siyasa. (Lami Ali)