A ranar 28 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin waje, da 'yan kasar Siriya da ke kasashen waje ta ba da sanarwa cewa, soke shirin hana sufurin makamai zuwa kasar Siriya ba zai yi amfani ga warware rikici na kasar Siriya ba.
A ranar 28 ga wata, babban hafsa-hafsoshin dakarun 'yantar da kasar Siriya Saleem Idlis ya bayyana cewa, duk da cewa, kungiyar EU ba za ta tsawaita lokacin yin takunkumin makamai kan kasar Siriya ba, amma wasu kasashe ba su tsara shirin samar da makamai ga bangaren adawa na Siriya ba. Don haka, wannan shawara wani zance ya zama wani ihu ne bayan hari. A wannan rana kuma, kakakin bangaren adawa na kasar Siriya Luay Safi ya bayyana cewa, ko da yake, bangaren 'yan adawa na Siriya ya yi maraba da soke wannan shirin da kungiyar EU ta yi, amma an makara, kuma ba zai canja halin da ake ciki ba.
Ministan harkokin wajen kasar Birtaniya William Hagueya ce, Birtaniya tana maraba da shawarar da kungiyar EU ta yanke, kuma wannan ya zama kashedin da aka yi wa mulkin Bashar al-Assa, amma Birtaniya ba za ta samar da makamai ga bangaren 'yan adawa nan da nan ba.
A ranar 28 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa Philippe Lalliot ya nuna cewa, Faransa ta yi maraba da kudurin da kungiyar EU ta yanka, kuma wannan shawara ce da aka yanke domin nuna goyon baya ga warware batun Siriya ta hanyar siyasa, makasudin tsai da wannan kuduri shi ne domin share fage ga taro na zagaye na 2 da za yi a wata mai zuwa a birnin Geneva.
Wasu Kasashen Australiya, Sweden, Finland da sauran kasashen Turai sun nuna adawa ga kudurin kungiyar EU, inda suka yi nuni cewa, matakin zai kawo karin mutuwa da jikkata ga Siriya, ba zai yi amfani ga aikin warware batun cikin ruwan sanyi ba.(Bako)