Gareth Ackerman, shugaban kungiyar "Pleiad Foundation" ya shaidawa kamafanin hadin gwiwar dillancin labarai na Afrika ta Kudu na SAPA cewa, kananan manoma zasu iyar kawo taimako sosai wajen kawar da matsalar karancin abinci da talauci a duniya.
A ranar Alhamis, kungiyar ta bada sanarwar fitar da wani sabon tsari dake da manufar taimakawa wajen shigar da kananan manoma dake gundumar Limpopo a kasar, ta yadda za'a samu wata hanyar kara samar da abinci.
Haka kuma kungiyar na bukatar bunkasa kwarewar manoman cikin tsarin kula, samar da abinci da kuma harkokin da suka shafi hukumar noma domin basu damar samun kudin shiga da na jari.(Maman Ada)