Hong Lei ya kara da cewa, yanzu tawagar bincike ta MDD ta tashi zuwa Sham. Kasar Sin ta yi fata, tare da imanin cewa, tawagar za ta yi tattaunawa da gwamnatin Sham daga dukkan fannoni, a kokarin gudanar da ayyukan bincike yadda ya kamata. Har wa yau kasar Sin na ganin cewa, kafin an gano gaskiyar lamarin, bai kamata ba a yi hasashe kan sakamakon binciken. Halin da ake ciki yanzu ya sake nuna muhimmanci da kuma bukatar gaggauta warware batun Sham a siyasance. Kasar Sin ta yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su yi iyakacin kokari tare domin shirya taro karo na biyu a birnin Geneva kan batun Sham cikin hanzari, da kuma kaddamar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi.(Tasallah)