Wani babban taro na bangarori uku da zai hada kasashen Angola, Afrika ta Kudu da jamhuriyyar demokaradiyar Congo DRC zai guduna a ranar Jumm'a mai zuwa a birnin Luanda, in ji ministan harkokin wajen kasar Angola a birnin Luanda.
Taron da zai hada shugaban kasar Angola Jose Eduardo Dos Santos, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma da kuma shugaban kasar DRC Joseph Kabila zai sanya a cimma wata yarjejeniya da za ta hasashen kafa wani tsarin bangarori uku domin rika tattaunawa kan muhimman batutuwan dake shafar wadannan yankuna.
Kasashen uku mambobi ne na kungiyar tarayyar kasashen kudancin Afirka SADC, da ta kasance wani gungu dake kunshe da kasashe goma sha biyar domin taimakawa warware matsaloli a cikin wadannan kasashe mambobi, kamar misalin matsalolin siyasa da na jama'a da ake fuskanta a DRC da Madagascar. (Maman Ada)