Kwanan baya, ministan kula da harkokin gona, bunkasuwar kauyuka da aikin kama kifi na kasar Angola Afonso Pedro Canga ya halarci bikin rufe aikin taya murnar sakamakon aikin kiwon dabbobi da aka shirya a lardin Benguela dake kudancin kasar inda ya nuna cewa, a halin da ake ciki, aikin noma da kiwon dabbobi sun samu cigaba cikin sauri a kasar, shi ya sa, gwamnatin kasar take shirin rage kuma daina shigo da naman shanu, kaji, kwan kaji da sauran amfanin gona da aikin kiwon dabbobi daga kasashen waje.
Afonso Pedro Canga ya ce, yanzu a wasu wuraren a kasar Angola, ana iya samar da isasshen naman shanu, kaji, kwan kaji da sauransu, amma, duk da haka, ko wace shekara, ana shigo da naman dabbobi da ya kai dajarar dalar Amurka miliyan 500 domin biyan bukatu a cikin kasar, a dalilin haka, gwamnatin kasar tana fatan za a cimma burin samar da isasshen wadannan kayayyaki ga bukatu a duk fadin kasar tare da fitar da wasu zuwa kasashen waje.
Afonso Pedro Canga ya kara da cewa, cigaban bunkasuwar aikin noma da kiwon dabbobi a kasar Angola tana da makoma mai haske, don nan gaba, gwamnatin kasar za ta sa kaimi kan aikin domin samar da hidima mai inganci a fannonin rancen kudi, samar da ruwan sha, lantakri da sauransu.(Jamila)