in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta yi kira ga kasashen yammacin duniya su cire takunkumi da aka sanyawa Zimbabwe
2013-08-19 09:46:15 cri

Taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar bunkasa kudancin Afirka (SADC), wanda aka yi a Lilongwe, babban birnin kasar Malawi, ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su cire takunkumi da suka dora kan kasar Zimbabwe, sakamakon nasarar da aka samu a zabe da aka gudanar a watan Yuli.

A fadin sanarwar bayan taron da aka bayar ranar Lahadi, shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar ta yanki sun nuna gamsuwa kan yadda aka gudanar da zaben, don haka ba su ga wani dalili da zai sa kasar Zimbabwe ta ci gaba da shan wahala ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, taron ya gamsu kan yadda aka gudanar da zabe cikin tsanaki da lumana a ran 31 ga watan Yulin shekarar 2013 a kasar Zimbabwe, inda kuma ya jadadda kiran a cire dukkan wani takunkumi da aka dorawa kasar.

Shugabar kungiyar SADC kuma shugabar kasar Malawi, Joyce Banda ta baiyana wa 'yan jarida a karshen taron cewa, talakawan kasar Zimbabwe ne ke wahala sakamakon dorawa kasar takunkumi.

Taron kungiyar da aka yi a Lilongwe ya kuma zabi sabbin jami'ai wa kungiyar da suka hada da Dr. Stergomena Lawrence Tax na kasar Tanzaniya a matsayin babban sakatare janar, inda ya maye gurbin Dr. Tomaz Augusto Salomao wanda wa'adinsa ya kare ranar Lahadi, kana Robert Mugabe shi ne mataimakin shugaba.

A fadin sanarwar, kasar Zimbabwe ita ce za ta karbi bakuncin taron shugabannin kasashen kungiyar SADC na gaba, a watan Agustan shekarar 2014. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China