in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen kungiyar SADC na zaman taron tattauna dangantakar tsaron shiyyar
2012-07-31 11:15:31 cri

Ministocin hukumar gamayyar cigaban kasashen kungiyar SADC kan harkokin siyasa, tsaro da dangantar tsaro na cikin wani zaman taro tun ranar Litinin a birnin Pretoria na kasar Afrika ta Kudu domin tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi tsaron shiyyar.

Ministar harkokin waje da dangantaka ta kasar Afrika ta Kudu, madam Maite Nkoana-Mashabane ta yi kira a cikin jawabinta na bude taron ga ofisoshin ministocin kasashen da su gudanar da ayyukan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin shiyyar.

Kasar Afrika ta Kudu ita ce a yanzu take shugabantar hukumar ta SADC a wannan karo kan siyasa, tsaro da dangantakar tsaro, kuma kasar Tanzania za ta karbi ragamar shugabanci a yayin taron kungiyar da za'a shirya a cikin watan Augustan gobe.

Kungiyar SADC wata babbar hukuma ce da a cikinta ya kamata mu cigaba da bayyana hangen zaman lafiyar shiyyar mu da bunkasuwarta, da kuma kasancewa wata hanyar dunkulewar shiyyar, in ji madam Nkoana Mashabane.

Hakazalika mahalartan taron za su tattaunawa kan batun shiga tsakani a kasar Madagascar, batun zabubuka da na tsaro a shiyyar. Haka kuma za su maida hankali kan yadda za'a iyar taimakawa kasashen mambobin kungiyar kan samun bunkasuwar tattalin arziki da kuma dunkulewa tare da sauran mambobin kasashen wannan kungiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China