Mahukuntan kasashen Angola da na Aljeriya sun amince da kafa wata tawagar masana, da za ta tsara managarcin shirin bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin albarkatun man fetir.
Da yake karin haske don gane da wannan batu, jim kadan da kammala ganawar wakilan bangarorin biyu ranar Talata 9 ga wata, ministan albarkatun mai na kasar Angola Jose Botelho de Vasconcelos, ya ce, kasarsa ta yanke shawarar bunkasa hadin gwiwar ne, ganin yadda Aljeriya ta rigaya ta yi nisa a wannan fanni.
Vasconcelos ya kara da cewa, dole ne kasar tasa ta yi koyi da irin kwarewar da Algeria ke da ita a dukkanin fannonin haka da sarrafa albarkatun mai. Daga nan sai ministan ya tabbatar da batun sanya hannu kan yarjejeniyar musayar fasaha tsakanin cibiyoyin horaswa a fannin na mai tsakanin kasashen biyu, shirin, a cewarsa, zai mai da hankali sosai ga muhimman kwasa-kwasai da kasashen ke bukatar samun kwararru a cikinsu. (Saminu)