Sakataren kungiyar Tomaz Salomao ne, ya bayyana hakan a madadin kungiyar ranar Asabar 16 ga watan nan. Salomao ya kuma yi kira ga al'ummar kasar da su rungumi wannan tsari na kaucewa hatsaniya, yayin zabukan majalissun dokoki, da na shugaban kasa dake tafe nan gaba cikin wannan shekara.
Sakataren kungiyar ta SADC, wanda kuma ya kasance cikin tawagar masu sanya ido yayin zaben, ya kara da cewa, abin da ya wakana a wannan lokaci, na haskaka irin nasarar da ake fatan samu, yayin zabukan kasar dake tafe.
Wannan dai daftarin dokoki da aka kada kuri'a a kan sa, shi ne irin sa na farko ga al'ummar kasar, wanda ke da nufin takaita wa'adin mulkin shugaban kasar zuwa shekaru 5 sau biyu kacal. Haka nan, an kada wasu kuri'un kan batun baiwa al'ummar kasar damar zama 'yan wasu kasashe, baya ga kasar tasu ta haihuwa, da kuma batun takaita hukuncin kisa.
Bugu da kari akwai batun karfafa ikon 'yancin mulkin kan kasar, da dai sauran muhimman batutuwa.
Muddin dai wannan daftarin kundin mulki ya samu amincewa, zai maye gurbin tsahon kundin da aka rubuta a birnin Landan cikin shekara ta 1980,tun kafin samun 'yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka. (Saminu Alhassan Usman)