in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke shugaban kungiyar 'yan uwan Musulmi ta kasar Masar
2013-08-20 14:21:50 cri
A ranar 20 ga wata, kamfanin dillancin labaru na kasar Masar na MENA ya ba da labarin cewa, 'yan sandan kasar Masar sun cafke Mohamed Badie, shugaban hukumar koli ta ba da jagoranci ga harkokin kungiyar 'yan uwan Musulmi a birnin Alkahira, hedkwatar kasar.

Jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta ruwaito kakakin ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Abdel-Fattah Osman yana cewa, yayin da aka cafke shi, Badie yana boye ne a wani gini na garin Nasr da ke arewa maso gabashin birnin Alkahira.

A ranar Laraba da ta gabata, rundunar tsaro ta kasar Masar ta dauki matakin korar masu goyon bayan Mohamed Morsi a wuraren da ke kusa da masallacin Rabaa El-Adaweya da ke garin Nasr, don kawo karshen zaman dirshan da suka yi har na tsawo makwanni 6.

Kamfanin dillancin labaru na Reutes ya kuma ba da labarin cewa, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Masar ta bayyana cewa, rundunar tsaro ta gudanar da aikin cafke Badie ne, bayan da masu gabatar da kara na kasar suka amince da hakan.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China