in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sassauci game da halin da ake ciki a kasar Masar
2013-08-20 14:44:14 cri

A ranar 19 ga wata, a titunan birnin alkahira hedkwatar kasar Masar da birnin Giza da ke kusa da shi, halin da ake ciki ya samu sassauci. Ayyukan yau da kullum sun fara farfadowa, har ma an samu cunkoson motoci a wasu tituna na birnin Giza.

Amma, har yanzu ana ci gaba da ganin shedar fito-na-fito tsakanin masu zanga-zanga da rundunar tsaro ta kasar suka haifar a wasu sassan biranen, haka kuma, rundunar tsaro ta jibge manyan motoci masu sulke kimanin 7 zuwa 8, sojoji na ci gaba da sintiri a wuraren.

Har yanzu, wasu shaguna na rufe, duk da cewa, ana farfado da zaman rayuwar al'umma. A wasu kananan shaguna, mutane na rige-rigen sayayya. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a cikin kwanaki da dama da aka yi rikici a wurin, dimbin mutane sun zauna a gidajensu, yanzu ganin halin da ake ciki ya samu sassauci, sannan su fito don yin cefane.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China