in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun mutu ko raunata a sakamakon ricikin da aka samu yayin da ake yin zanga-zanga a kasar Masar
2013-08-17 16:26:09 cri
A ranar 16 ga wata, magoyan bayan Mahmoud Morsy sun yi zanga-zanga a birane da dama dake kasar Masar, kuma sun yi rikici tare da 'yan sanda da mazaunan dake wuraren. Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta bayar, an ce, mutane a kalla 48 sun mutu a sakamakon rikice-rikicen da aka samu a wannan rana, kana mutane 436 sun ji rauni. Kasa da kasa sun ci gaba da lura kan halin da ake ciki a kasar Masar, kuma sun yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su kwantar da hankali da kuma dakatar da tada rikici.

Kakakin jam'iyyar 'yan uwa musulmi wato "Muslim Brotherhood" ya bayyana a ranar 16 ga wata cewa, kungiyar za ta yi zanga-zanga cikin lumana a kowace rana a fadin kasar. Majalisar ministocin kasar ta bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ta yi kira ga dukkan jama'ar kasar da su kiyaye dinkewar dukkan kasar da kuma magance warewar kasar. Sanarwar ta yi kira ga membobin kungiyar 'yan uwa musulmi da sunan "'yan ta'adda". Bisa labarin da hukumar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta bayar, an ce, 'yan sandan kasar sun kama magoyan bayan Mahmoud Morsy da mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi fiye da dubu daya.

Babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Catherine Ashton ta bayar da wata sanarwa a ranar 16 ga wata, inda ta bukaci wakilan kasashe mambobin kungiyar EU da su tattauna kan matakan da ya kamata kungiyar ta dauka wajen tinkarar halin da ake ciki a kasar Masar.

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya buga waya ga firaministan kasar Ingila David Cameron da firaministan kasar Italiya Enrico Letta, inda suka samu daidaito kan cewa, aikin dake gaban kome a kasar Masar shi ne kawo karshen rikici, girmama hakkin dan Adam da kuma mayar da yin shawarwari a dukkan kasar.

Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya buga waya ga ministan harkokin waje na kasar Masar Fahmy a ranar 16 ga wata, inda ya ce, Sin ta sa lura sosai kan halin da ake ciki a kasar Masar, kuma tilas ne bangarori daban daban na kasar Masar su yi la'akari da moriyar kasar da ta jama'a, su kiyaye hakuri don magance tsanantar halin da aka shiga. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China