Daga Litinin 19 ga wata zuwa Talata 20 ga wata ne, aka gudanar da babban taron da ya shafi aikin yada labarai na kasar Sin a birnin Beijing, hedkwatar kasar, inda shugaban kasar Sin, Mista Xi Jinping, ya bukaci a tsara wasu sabbin fasahohi wajen yada labarai ga kasashe daban daban, don bayyana labaran da suka shafi Sinawa yadda ya kamata, da kokarin yada muryar kasar Sin.
A cewar Mista Xi, ya kamata a sanya jama'ar duniya su kara sanin kasar Sin. Ganin yadda Sinawa ke da al'adu masu dimbin tarihi, don haka dole ne jama'ar kasar su ci gaba da raya wadannan al'adun kasar masu dogon tarihi a nan gaba. (Bello Wang)