in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan Pakistan Nawaz Sharif
2013-07-05 10:52:29 cri

Ran 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ganawa tare da firaministan kasar Pakistan Nawaz Sharif a babban otel na Diaoyutai, dake birnin Beijing na kasar. Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin da Pakistan abokan arzikin juna ne kuma makwabta ne nagari, kana zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu na da inganci sosai, kuma suna hadin gwiwa a dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Ya ce, 'Ya kamata mu ci gaba da karfafa zumuncin gargajiya tare kuma da inganta harkokin hadin gwiwar dake tsakaninmu.' Firaminista Nawaz Sharif ya nuna cewa, jama'ar Pakistan sun darajanta zumuncin 'yan uwantaka da ke tsakaninsu da jama'ar kasar Sin. Ya ce, Pakistan ta nuna matukar godiya ga goyon baya da taimako da kasar Sin take ba ta cikin dogon lokaci, kana kasar Sin ita ce kasa ta farko da ya kai mata ziyara, bayan kama aikin sabon firaministan kasar, dalilin haka shi ne domin inganta dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu. A halin yanzu kuma, Pakistan na dukufa wajen raya tattalin arzikinta, da kiyaye yanayin tsaro a kasar, kuma tana son karfafa hadin gwiwa da kasar Sin bisa fannoni daban daban. Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan harkokin kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya yayin ganawarsu. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China