in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci a zurfafa kokarin yin kwaskwarima a bayyane
2013-07-23 21:00:41 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a zurfafa kokarin da ake yi na kwaskwarima da kuma bayyana ingantacciyar hanyar tattalin arziki don a samu warware manyan matsalolin da ake fuskanta a wannan bangaren.

Mr. Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya yi fadi hakan ne lokacin rangadin da ya kai a lardin Hubei da ke tsakiyar kasar daga ranar Lahadi 21 zuwa ranar Talata 23 ga wannan watan.

Shugaban ya bayyana kokarin kwaskwarimar da ake yi da cewar wata dabara ce mai kyau, kuma ana cikin yanayin shi ne tare da bullo da sabbin dabaru, a ko wane mataki na gwamnati da kuma ayyukan tattalin arziki.

Ya lura da cewa, hanyar da za'a bi a shawo kan wadannan kalubale da tangarda da kasar Sin ke fuskanta shi ne a zurfafa kokarin yin kwaskwarima yadda ya kamata.

Mr. Xi sai dai ya jaddada cewa, dole ne mahukunta su saki zuciyarsu su yi aiki tukuru domin samo gaskiya daga cikin bayanan da za'a fitar domin samar da daidaito tsakanin kwaskwarima, cigaba da karko.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China