in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya ce wajibi ne sojojin kasa sun bi shugabancin JKS.
2013-07-30 10:04:25 cri

Shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya, Xi Jinping ya jaddada bukatar dake akwai na tabbatar da cewa rundunar sojin kasar sun bi shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sau da kafa.

Mr. Xi ya yi wannan furucin ne lokacin wani rangadin cibiyar sojin dake Beijing fadar gwamnatin kasar a ranar Litini 29 ga watan nan.

Ziyarar ta zo ne kwanaki kadan kafin ranar Sojin kasar wadda za ta fado a ranar 1 ga watan Agusta, kuma ita ce ta cika shekaru 86 da samar da rundunar ta sojojin 'yantar da al'ummar kasar PLA.

A madadin kwamitin tsakiya da kuma kwamitin aikin sojan tsakiya na JKS, shugaban ya isar da gaisuwa da sakon fatan alheri ga sojoji dake wannan rundunar da ma wadanda suke sauran sassa a kasar.

Lokacin rangadin na shi, shugaban ya gana da manyan jami'an soji, sannan ya saurari rahoton ayyukan rundunar. Haka kuma ya ziyarci ofishin sadarwar su, inda ya tattauna da sojojin game da ayyukan su, karatun su da kuma yanayin rayuwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China